Friday, January 11, 2019

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari A Yau Yayi Wani Jawabi Mai Ratsa Jiki



  SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YAYI JAWABI MAI RATSA JIKI, YAU A ABUJA

 Ya 'yan uwana yan Nigeria !!! Ubangiji Ya san zuciyata, bata dawani buri daya wuce na saita kasata Nijeriya, a tafarkin da zakuji dadi nan gaba. Domin kune matasa masu tasowa.

 Akwai tsananin wahala a mulki, yayin da kake koqarin kawo canji a kasa Kamar Nigeria, Zaka hadu da Kalubale Kala Kala mai Wahalar gaske. Muna iya koqarinmu a yanzu domin muga komai ya daidaita a kasarmu. Kuma na tabbata koda abokan hamayyarmu, sunsan cewa muna iyakar kokarimu don ganin mun daura kasarmu a turbar data dace.

 Amman nasan wasu Daga cikinsu suna ganin Munyi laifi, sakanmakon hana ha'inchi da almundahana da dukiyar al'umma.

 Ga wadannan yan siyasa, masu sha'awar abarsu suyi wadaka da kudin governmenti, mun san bazasu ta6a yafe mana ba. Ko kuma suga kokarinmu, Bazasu ganiba!!! Bazasu ganiba!!!.

 Domin anasu tunanin bamu Kyautata musuba, munyi musu laifi.
Laifin kuwa shine:- Mun toshe musu duk wassu hanyoyin dasuke bi wajen sace dukiyar al'ummah. Dominsu basu da wata damuwa, illa abarsu suyi badakala da dukiyar kasa.
Sun yarda da haka koda kasarnan zata lalace, domin suntara kudaden da gidaje a ketare.
Sun shirya tsaf da karfinsu domin wargaza shirin da muka soma na saita wannan kasar tamu.
Basuda damuwa koda da kwayar zarra, dangane da damuwar mutanen kasar nan .
Bamu da wani za6i, Illa za6in mutanan

 Yan Nijeriya, idan sun amince da kokarinmu, zasu iya sake za6anmu a karo na biyu domin cigaba daga inda muka tsaya. Hakanne zai amfanemu Baki daya.
Idan kuma baku aminta damu ba, zaku iya komawa garesu (wato yan jari hujja ). Domin wargaza muku rayuwar ku ta nan gaba, dama kasar baki daya.

 Amma na tabbas zaku tuna cewa na fada muku gaskiya ko bayan Raina, kuma nayi iya kacin kokarina domin naga kasarmu ta hau turban gaskiya, da rikon amana, Za6i ya rage naku yan Nigeria, domin kasarmu.
Allah yasan zuciyata da abinda ke cikinta, inayin wannan maganane tsakanina da Allah.
ALLAH YA TAIMAKI KASATA DA AL'UMMARMU BAKI DAYA.

Hediquatar Tsaro Ta Nigeria Ta Kalubalanci Yan Jarida.



 Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi kira ga ‘yan jaridar kasar da su rika bai wa hukumomin tsaro hadin kai yayin da suke gudanar da ayyukansu.
A cewar Darektan yada labarai a hedkwatar tsaron kasar, Brigadier General John Agim, yayata labaran da ke fitowa daga bangaren mayakan Boko Haram tamkar taimakawa ayyukan ta’addanci ne.
“Duk dan jaridar da ke rawar jiki wajen aika rahoto kan abin da Boko Haram ta yi ko ta ce, ko kana so ko ba ka so, ya zama kana masu aiki kenan.” In ji Agim.
Ya kara da cewa, hedkwatar tsaron ta Najeriya na matukar bukatar hadin kan kowa da kowa wajen yaki da masu ta da kayar baya a rewa maso gabashin Najeriya.
“Saboda wannan yaki ne mai wuyar sha’ani, muna yakar wadanda sun san mu amma mu ba mu san su ba.” In ji Agim.
Wadannan kalamai na hedkwatar tsaron na zuwa ne kwanaki kadan bayan da sojojin Najeriya suka kai wani samame a ofishin gidan jaridar Daily Trust da ke Abuja, bayan wani labari da kamfanin ya wallafa.
Sojojin sun zargi gidan jaridar da wallafa wasu bayanai da suka jefa harkar tsaron kasar cikin hadari.
Ko da yake, samamen da aka kai wa jaridar ta Daily Trust ya janyo aka yi ta sukar jami’an tsaron a ciki da wajen Najeriya, amma masana a fannin tsaro sun ce akwai bukatar ‘yan jarida su rika takatsatsan wajen wallafa bayanan tsaro.
“Irin wadanan labarai a duk lokacin da aka yi su, ya kamata a rika tace su a tabbatar da cewa ba su yi karo da abubuwa na tsaro ba.” In ji Air Commander Ahmed Tijjani Babagamawa mai ritaya, wanda kan yi sharhi kan tsaro.
Tun daga shekarar 2009, Najeriya ke fama da hare-haren ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, musamman a arewa maso gabashin kasar
Ayyukan kungiyar ya salwantar da dubban rayukan jama’a a kasar ta Najeriya da makwabtanta.
A shekarar 2015 an samu lafawar rikicin, amma a baya-baya nan, mayakan kungiyar ta boko Haram, sun kara zafafa hare-haren da suke kai wa.
Wasu bayanai sun yi nuni da cewa yanzu haka wasu garuruwa akalla shida ciki har da garin Baga a yankin jihar Borno sun sake fadawa hannun mayakan, amma dakarun na Najeriya sun musanta wannan ikrari.

Thursday, January 10, 2019

Yan sanda sun harbe wasu direbobi 2 a kogi bisa laifin kin basu cin hanci


kubiyo domin jin yadda lamarin ya wakana:



 Wasu yan sanda dake a pariya dake kan hanyar Fufore a jihar Adamawa sun harbe wasu fasinjoji biyu domin rashin amincewa da suka nuna akan kar bar rashawa daga direbansu.

  Majiyarmu na cewa daga cikin fasinjojin biyu da aka harba acikin motar Allah yayiwa daya cikawa nan ake bada jimawa ba p, yayinda shikuma dayan yake jinya a asibiti, sunansa malam Umar wanda yake jinya a asibitin Jimeta.

 Aminiya ta fahimci cewa wannan lamarin ya faru ne a Ibro Motor park wanda ke fuskantar kasuwar lokoja. shugaban reshen kungiyar tarayyar kasa ta ma'aikatan sufuri na hanya [NURTW], mai suna Ibrahim yakubu, yace matsalar ta fara ne lokacinda yan sanda suka dakatar da daya daga ciki yan san da a wani wuri yadda zango a kan hanya Lokoja-Okene ya basu cin hanci.

Kamar yadda kwamishinan ya fada, ya shaidawa yan sandan cewa ba shi da abinda zai basu a wancen lokacin kuma ya cigaba da tafiyar shi zuwa Lokoja. sai dai ya ce yan sandan wadanda basu yarda ci gaban ba sun bawa direban damar yin zabi a filin Ibro Motor park inda suka ce direban ya da katar da motarsa ya gudu zuwa wurin shakataw don neman mafaka.

 Yakubu yace yan sanda biyu sun gudu bayansa a cikin motar, yayinda shugaban kungiyar, wanda akafi sani da inspector Mohammaed Usman, ya dawo cikin motar.muna zaune awurin shakatawar wurin karfe 11am sai muka fara jin wani motsi kadan,abun mamaki shine munga daya daga cikin direbobimmu ya gudu zuwa ofishi sannan mukaga yan sanda biyu sun bishi, mun gayamasa cewa muna daukar motar zuwa wajen shakatawa kuma ya bi mu acki a lokacinda muke zuwa wajen ofishin yan sanda mun gaya masa cewa mun riga mun magance alamarin tare da sauran yan sanda biyu.

Lokacinda yaji haka sai yayi fushi ya fito da bindiga ya harbe shi a kasa ya yinda yake ci gaba da harbe har bensa. koma dai mi kenan jami ai na musamman sunanan suna bicike  


NLC: Anya babu Yaudara A Kwamitin Da Gwamnatin Tarayya Takafa




 An ci gaba da murza gashin baki tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar 'yan kwadago wato NLC game da karin albashin ma’aikatan Najeriya.
 A jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamiti dake karkashin sanannen masanin tattalin arziki Mr Bishmak Riwane, wanda kuma aka debawa kwanaki talatin [30] domin yin nazari da kuma ya mika rahoton karin albashin na ma'ikata.
 A jawabinsa wajen kaddamar da wannan kwamitin, shugaba Buhari yace akwai bukatar yin garon bawul ga daukacin albashin ma’aikata, ko kuma dai dai ta su domin tafiya tare.
 Tuni dai kungiyar kwadago ta kasa tayi wantsakalar da wannan kwamitin, tana mai cewa, wata dabara ce ta gwamnati na jan kafa a dai dai lokacin da zaben kasa ya karaso domin ta kiyin karin albashin.
 Ra’ayin wasu 'yan Najeriya game da shirin karin albashin ko akasin hakan ya banbanta. Wasu na ganin gaskiya mafi karancin albashi na Naira dubu goma sha takwas [#1800] yayi kadan a kasar nan wasu kuma abin basu cewa komai.
 Shima wani malamin, cewa yayi akwai bukatar gwamnati ta kara albashin, domin biyan bukatun ma’aikata, waddanda ke zaune a gidajen haya ko biyan kudin makaranta yara ya za suyi? Ai ko sabon albashin na naira #30,000 sai ayi maleji domin kuwa abubuwa sun tashi goron zabuwa ba kamar yadda aka sansu ada ba.
 Sauda yawa dai wasu na ganin idan aka kara albashin, hakan zai haifar da tsadar kayan masarufi, hasashen da wani masanin tattalin arziki Malam Isa Imam, yace ba gaskiya bane; yace koda yake za’a samu karin farashin kaya, amma hakan ba zai taka kara ya karya ba, domin tashin kayan bazai dore ba kamar yadda ake gani a wasu kasashe da basu da karfin tattalin arziki.
 Yanzu dai abun jira a gani shine ko rahoton da wannan kwamitin zai mikawa  gwamnatin, ana saura mako daya zaben kasa, zai yi tasiri ga ma’aikatan na samun karin albashinsu akan kari, kafin zaben kasa?

"Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Hudu A Katsina Har Lahira"



 Wasu yan ta'adda  da ba'a san ko suwanene ba sun kashe sun kashe mutum hudu a wani kauye, Majiyar mu na cewa yan bindigar sunje ne a kauyen yar santa dake karamar hukumar kankara ta jihar Katsina.

 Bayanai sunnuna cewa tuni dai akayi janaizar mutanen da yan ta'addar suka kashe kamar yadda addinin musulinchi ya shar'anta, a jiya larabane aka ruhosu.

 Yayinda jami'in watsa labarai na rundunar 'yan sanda na jihar Katsina, sp Gambo Isah ya tabbatar da lamarin ya kuma ce ya zuwa yanzu lokacinda aka hada wannan rahoton ba shida cikakken bayanin yadda lamarin ya auku.
  
 Majiyar mu ta bayyana mana cewa, yan ta'addan sun kai hari a kauyenne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata a dai dai lokacinda mutanen garin suke dawowa daga babbar kasuwar garin Kankara.

 An kuma bayyana mana cewa yan ta'addan sun shigane akan babura kuma nan take suka fara harbe-harbe da manyan bindigogi a kauyen abunda yasa  hankalin jama'a kenan ya tashi suka fara guje-guje wurare daban daban. Mutun hudun da suka mutu' harbin bindiga ne da yan ta'addan yayi sanadiyyar rasa rayuwarsu nan take.

 ''yan ta'addan sun kuma dawo washe gari ranar laraba kenan a dai dai lokacinda ake yin jana'izar wanda suka rasun, inda 'yan sintiri suka fatattakesu''

Daya daga cikin mutanen garin ya kuma ce, da safiyar yau dai dai lokacinda muke jana'izar wadanda suka rasun yan ta'addan sun sake dawowa sai dai yan sintirin garinmu suka fatattakesu.

 Yayinda jami'in watsa labarai na yan sanda ya kuma ce tuni aka tura jamia'an tsaro a kauyen don bayar da kariya.
sp Isah yace ''lallai yanzu mutanenmu na nan don shawo kan lamarin''.


yadda wani jirgin kasa yayi hadari a lagos

       
                                         

     Shidai wannan jirgin kasan mai tarako 17 ya samu hadari ne a kan hanyarsa inda ya taso daga unguwar llu yabi ta oshodi zuwa wurin ebuta mita.

        A inda yayi hadarin daa misalin karfe bakwai 7 na safiyar yau kuma yana dauke ne da mutane da kuma kayayyaki.
         
        shidai wannan hatsarin ya afku ne a wata unguwar da ake kira da mangora Agegen jihar lagos a Nigeria a inda ya raunata mutane da dama kamar yadda majiyarmu ya tabbatar.

       Majiyarmu ya tabbatar mamu da cewar a lokacinda suka zanta da commander na hukumar kare hadura ta kasa wato (FRSC), Emma Fekoye ya tabbatar mamu da afkuwar lamarin, sai dai ya tabbatar mamu da cewar a lokacinda da hadarin ya afku babu wanda ya mutu amma sai dai an samu raunuka da dama.
       
     Fasinjojin jirgin kasan ssun fito sun fito da kansu a inda suka karasa a kasa  don su sami abun hawa  domin jirgin ya toshe hanyar da mutane ke wucewa a unguwar.

     wani daga cikin wanda majiyarmu suka zauna da shi wanda ake kira da Ikechukwu Nwachuku  ya bayyana ma majiyarmu cewar jirgin ya samu hadari ne a wani wuri a inda titin ya fashe a sanadiyyar hakane ya kauce hanyarsa.

        Bugu da kari jami'an bada agaji na gaggawa sun halarta a wajen da lamarin ya afku a inda suka taimakawa wadanda suka jikkata kuma suka cigaba da kyaran hanyar yadda jama'a zasu sami saulin sufiri.

  



   

Sunday, January 6, 2019

An gano jigin yakin daya bace a barno dakaru biyar na ciki sun mutu

An gano jirgi yakin daya bace a barno dakaru 5 na ciki sun mutu


Matukan jirgi saman sojojin Nigeria guda biyu tareda sojojin sama guda ukku ne aka tabbatar da mutuwarsu. A batsari jirgin yakin mai saukar ungulu wanda akafi sani da jet bombee, wanda ya aiku a farin damasak acikin jihar barno a ranan larabannan
  Wadanda suka gamu da ajalinsu ta dalilin wannan hatsarin sun kunshi
Kwamanda laftanar Perowi Jacob da laptanar kaltho kiluofas sauran sune sajan Auwal Ibrahim da bakaniken jirgin wato las kofur Adamu Nura, trader Meshack Ismail
 Majiyar mu na cewa A sanarwar da rundunar sojojin sama ta Nigeria wato (NAF) ta first a ranar Albania ta hannum daraktan dake hudda da juma'a na rundunar Air commandor Ibikunle Daramola, ta tabbatar da cewa sauran wadanda suka kubuta daga hatsarin an kawo su Maiduguri
 Yayinda muka samu rahoton cewa wanna jirgin yakin mallakar Nigeria ne wanda aka tura wurin yaki don yaki da Boko Haram yayinda ya bace a fagen fa ma.
 Har iya rundunar ta sake bayyana mana cewa jirgin yakin ya bata ne da misalin karfe 7:45 na yammacin ranar laraba, Wanda aka tura shi domin dafawa sojojin Nigeria dake aikin Samar da tsaro a karkashin bataliya ta 145 dake garin Damasak wanda ke arewacin jihar Borno wanda kuma har kawowa yanzu muna neman musabbabin wannan fadowar jirgin saboda rashin kyawun yanayi.
 Amman dazarar lamura sun natsa zamu gayawa jama'a cikakken bayanin yadda al'amarin ya afku injishi.