Wasu yan ta'adda da ba'a san ko suwanene ba sun kashe sun kashe mutum hudu a wani kauye, Majiyar mu na cewa yan bindigar sunje ne a kauyen yar santa dake karamar hukumar kankara ta jihar Katsina.
Bayanai sunnuna cewa tuni dai akayi janaizar mutanen da yan ta'addar suka kashe kamar yadda addinin musulinchi ya shar'anta, a jiya larabane aka ruhosu.
Yayinda jami'in watsa labarai na rundunar 'yan sanda na jihar Katsina, sp Gambo Isah ya tabbatar da lamarin ya kuma ce ya zuwa yanzu lokacinda aka hada wannan rahoton ba shida cikakken bayanin yadda lamarin ya auku.
Majiyar mu ta bayyana mana cewa, yan ta'addan sun kai hari a kauyenne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata a dai dai lokacinda mutanen garin suke dawowa daga babbar kasuwar garin Kankara.
An kuma bayyana mana cewa yan ta'addan sun shigane akan babura kuma nan take suka fara harbe-harbe da manyan bindigogi a kauyen abunda yasa hankalin jama'a kenan ya tashi suka fara guje-guje wurare daban daban. Mutun hudun da suka mutu' harbin bindiga ne da yan ta'addan yayi sanadiyyar rasa rayuwarsu nan take.
''yan ta'addan sun kuma dawo washe gari ranar laraba kenan a dai dai lokacinda ake yin jana'izar wanda suka rasun, inda 'yan sintiri suka fatattakesu''
Daya daga cikin mutanen garin ya kuma ce, da safiyar yau dai dai lokacinda muke jana'izar wadanda suka rasun yan ta'addan sun sake dawowa sai dai yan sintirin garinmu suka fatattakesu.
Yayinda jami'in watsa labarai na yan sanda ya kuma ce tuni aka tura jamia'an tsaro a kauyen don bayar da kariya.
sp Isah yace ''lallai yanzu mutanenmu na nan don shawo kan lamarin''.

No comments:
Post a Comment