Thursday, January 10, 2019

NLC: Anya babu Yaudara A Kwamitin Da Gwamnatin Tarayya Takafa




 An ci gaba da murza gashin baki tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar 'yan kwadago wato NLC game da karin albashin ma’aikatan Najeriya.
 A jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamiti dake karkashin sanannen masanin tattalin arziki Mr Bishmak Riwane, wanda kuma aka debawa kwanaki talatin [30] domin yin nazari da kuma ya mika rahoton karin albashin na ma'ikata.
 A jawabinsa wajen kaddamar da wannan kwamitin, shugaba Buhari yace akwai bukatar yin garon bawul ga daukacin albashin ma’aikata, ko kuma dai dai ta su domin tafiya tare.
 Tuni dai kungiyar kwadago ta kasa tayi wantsakalar da wannan kwamitin, tana mai cewa, wata dabara ce ta gwamnati na jan kafa a dai dai lokacin da zaben kasa ya karaso domin ta kiyin karin albashin.
 Ra’ayin wasu 'yan Najeriya game da shirin karin albashin ko akasin hakan ya banbanta. Wasu na ganin gaskiya mafi karancin albashi na Naira dubu goma sha takwas [#1800] yayi kadan a kasar nan wasu kuma abin basu cewa komai.
 Shima wani malamin, cewa yayi akwai bukatar gwamnati ta kara albashin, domin biyan bukatun ma’aikata, waddanda ke zaune a gidajen haya ko biyan kudin makaranta yara ya za suyi? Ai ko sabon albashin na naira #30,000 sai ayi maleji domin kuwa abubuwa sun tashi goron zabuwa ba kamar yadda aka sansu ada ba.
 Sauda yawa dai wasu na ganin idan aka kara albashin, hakan zai haifar da tsadar kayan masarufi, hasashen da wani masanin tattalin arziki Malam Isa Imam, yace ba gaskiya bane; yace koda yake za’a samu karin farashin kaya, amma hakan ba zai taka kara ya karya ba, domin tashin kayan bazai dore ba kamar yadda ake gani a wasu kasashe da basu da karfin tattalin arziki.
 Yanzu dai abun jira a gani shine ko rahoton da wannan kwamitin zai mikawa  gwamnatin, ana saura mako daya zaben kasa, zai yi tasiri ga ma’aikatan na samun karin albashinsu akan kari, kafin zaben kasa?

No comments:

Post a Comment