
Shidai wannan jirgin kasan mai tarako 17 ya samu hadari ne a kan hanyarsa inda ya taso daga unguwar llu yabi ta oshodi zuwa wurin ebuta mita.
A inda yayi hadarin daa misalin karfe bakwai 7 na safiyar yau kuma yana dauke ne da mutane da kuma kayayyaki.
shidai wannan hatsarin ya afku ne a wata unguwar da ake kira da mangora Agegen jihar lagos a Nigeria a inda ya raunata mutane da dama kamar yadda majiyarmu ya tabbatar.
Majiyarmu ya tabbatar mamu da cewar a lokacinda suka zanta da commander na hukumar kare hadura ta kasa wato (FRSC), Emma Fekoye ya tabbatar mamu da afkuwar lamarin, sai dai ya tabbatar mamu da cewar a lokacinda da hadarin ya afku babu wanda ya mutu amma sai dai an samu raunuka da dama.
Fasinjojin jirgin kasan ssun fito sun fito da kansu a inda suka karasa a kasa don su sami abun hawa domin jirgin ya toshe hanyar da mutane ke wucewa a unguwar.
wani daga cikin wanda majiyarmu suka zauna da shi wanda ake kira da Ikechukwu Nwachuku ya bayyana ma majiyarmu cewar jirgin ya samu hadari ne a wani wuri a inda titin ya fashe a sanadiyyar hakane ya kauce hanyarsa.
Bugu da kari jami'an bada agaji na gaggawa sun halarta a wajen da lamarin ya afku a inda suka taimakawa wadanda suka jikkata kuma suka cigaba da kyaran hanyar yadda jama'a zasu sami saulin sufiri.
No comments:
Post a Comment