SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YAYI JAWABI MAI RATSA JIKI, YAU A ABUJA
Ya 'yan uwana yan Nigeria !!! Ubangiji Ya san zuciyata, bata dawani buri daya wuce na saita kasata Nijeriya, a tafarkin da zakuji dadi nan gaba. Domin kune matasa masu tasowa.
Akwai tsananin wahala a mulki, yayin da kake koqarin kawo canji a kasa Kamar Nigeria, Zaka hadu da Kalubale Kala Kala mai Wahalar gaske. Muna iya koqarinmu a yanzu domin muga komai ya daidaita a kasarmu. Kuma na tabbata koda abokan hamayyarmu, sunsan cewa muna iyakar kokarimu don ganin mun daura kasarmu a turbar data dace.
Amman nasan wasu Daga cikinsu suna ganin Munyi laifi, sakanmakon hana ha'inchi da almundahana da dukiyar al'umma.
Ga wadannan yan siyasa, masu sha'awar abarsu suyi wadaka da kudin governmenti, mun san bazasu ta6a yafe mana ba. Ko kuma suga kokarinmu, Bazasu ganiba!!! Bazasu ganiba!!!.
Domin anasu tunanin bamu Kyautata musuba, munyi musu laifi.
Laifin kuwa shine:- Mun toshe musu duk wassu hanyoyin dasuke bi wajen sace dukiyar al'ummah. Dominsu basu da wata damuwa, illa abarsu suyi badakala da dukiyar kasa.
Sun yarda da haka koda kasarnan zata lalace, domin suntara kudaden da gidaje a ketare.
Sun shirya tsaf da karfinsu domin wargaza shirin da muka soma na saita wannan kasar tamu.
Basuda damuwa koda da kwayar zarra, dangane da damuwar mutanen kasar nan .
Bamu da wani za6i, Illa za6in mutanan
Yan Nijeriya, idan sun amince da kokarinmu, zasu iya sake za6anmu a karo na biyu domin cigaba daga inda muka tsaya. Hakanne zai amfanemu Baki daya.
Idan kuma baku aminta damu ba, zaku iya komawa garesu (wato yan jari hujja ). Domin wargaza muku rayuwar ku ta nan gaba, dama kasar baki daya.
Amma na tabbas zaku tuna cewa na fada muku gaskiya ko bayan Raina, kuma nayi iya kacin kokarina domin naga kasarmu ta hau turban gaskiya, da rikon amana, Za6i ya rage naku yan Nigeria, domin kasarmu.
Allah yasan zuciyata da abinda ke cikinta, inayin wannan maganane tsakanina da Allah.ALLAH YA TAIMAKI KASATA DA AL'UMMARMU BAKI DAYA.

No comments:
Post a Comment